DOLE MU CIGABA DA DAGA MURYA CEWA AREWA SU FARKA: UMAR FARUQ

0

A watan da ya gabata ne dimbin matasa suka fito a kan titunan kasar musamman a arewacin kasar domin nuna kyamar su ga abubuwan da suke faru a arewacin kasar musamman a bangaren tsaro da tsadar rayuwa.

Hakazalika matasan sunyi ta amfani da kafar sadarwa na zamani iron su tiktok, Facebook ,Twitter da Instagram ta hanyar daga kwali da rubutu masu nuna rashin amincewar su da Munnar ranar samun yanci.

Sai dai abin tambayar anan shin hakar ta cimma ruwa, kokuma yinkurin nasu ya Kare a banza.

Wannan shi tambayar da wani matashi Umar faruq ya amsawa wakilin mu Nasir da cewa

Tabbas wannan yinkurin nasu bai Kare a banza ba domin kuwa Koda Gwamnati bata fito ta ce komai ba tabbas wadanda da a baya Basu Ankara dacewa babu wani yanci da muke da shi harda zamu yiwa shagali ba yanzu sun fahimci hakan.

Hakazalika matasan arewa kaso talatin da biyar zuwa arba’in sun fara gane cewa a na amfani da sune lokacin siyasa bayan anyi nasara kuma ayi watsi da su ba tare da sunci moriyar wahalan su ba,Wanda yace hakan zaiyi matuka tasiri da amfani a zabe na gaba

Daga karshe Umar yayi Kira ga matasan arewa Kada suyi kasa a guiwa su cigaba da yada manufar su har sai hakan su ta cimma ruwa ku ya tabbatar da cewa babu nasara dake zuwa a rana Daya dole sai an daure wajen yada manufa ta hanya lumana

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.