KA NEMI SANA’A SIYASA BATA KAMACE KA BA OBI,CEWAR TUNIBU
CEWAR TUNIBU: Gwamnatin Najeriya ta kalubalanci Peter Obi
Gwamnatin Najeriya ta kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023 da ya gabata da cewa ya rungumi salon yakin neman zabe na amfani da batutuwan kawo ci gaba, a maimakon yin amfani da addini da kabilanci kamar yadda ya yi a zaben da ya wuce.
Hakazalika Gwamnatin ta ce ta rasa yadda Peter Obi wanda ta kira mai kwaikwayon abin da ya ga wani ya yi, jam’iyyarsa ta LP suka hakikancewa kansu cewa su ne suka ci zaben da a kayi za a zahiri ya zo na uku.
Gwamnatin na mayar da martani ne a wani taron manema labarai da Peter Obi ya gudanar ranar a ranar Litinin inda ta zarge shi da zubar da mutuncin bangaren shari’a.
Shi dai Obi ya ce kotun koli ta yi watsi da shaida ta yankan shakku, kamar kin vin amfani da dokokin zaɓe ne wanda ya ce INEC ta yi, kuma abu ne da ya ce bai kamata hukumar zaɓen ta yi wasa da shi ba.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce dan takarar na jam’iyyar LP a zaben da ya wucen, yayin taron manema labaran da ya gudanar, tamkar Atiku Abubakar, ya yi kokarin zubar da mutuncin Kotun Koli da hukumar zabe ta INEC saboda a cewarta, don kawai ba su ayyana shi wanda ya ci zaben ranar 25 ga watan Fabrairu ba.
haka kuma ta ce kamata ya yi a zurfafa nazari kan babban mafarkin Peter Obi, wanda ya yi imanin da cewa zai iya cin zabe ta hanyar gudanar da yakin neman zabe mafi haddasa gaba da janyo rarrabuwar kawuna da ya gwara kan alumar Kiristoci da Musulmai da kuma wannan kabila da wata a kasa mai yawan kabilu da yawan addinai kamar Najeriya.
Sanarwar da Babban Mashawarcin Tinubu kan harkar yada labarai Mr. Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Peter Obi ya yi kokari ba tare da nasara ba wajen tunzura ‘yan Najeriya da karairayi da gugar zana, sannan ta zarge shi da yin tufaka da warwara.
Gwamnatin Tinubu ta ce Obi ya amfana da hukunce-hukuncen kotuna a baya amma a yanzu yana bata suna kotun saboda hukuncinta bai yi masa dadi ba.