An nada Fabregas kociyan Como ta kasar Italiya

An nada Fabregas kociyan Como ta Italiya na rikon kwarya

0

An nada Fabregas kociyan Como ta Italiya na rikon kwarya

 

Tsohon dan wasan Arsenal da Chelsea da Barcelona Cesc Fabregas ya zama  kociyan Como ta kasar Italiya a matakin rikon kwarya.

Fabregas, tsohon Dan wasa mai shekara 36, wanda zai fara aikin horar da wasan tamaula a karonsa na farko, A yayin da ya maye gurbin Moreno Longo.

Ya buga wa kungiyar wasa 17 a bara, wadda take Serie B, daga nan ya yi ritaya dagawasan kwallon kafa ya zama kociyan karamar kungiyar.

Wasan farko da Fabregas zai ja ragama sa shi ne wanda za su karbi bakunci Feralpisalo a ranar 25 ga watan Nuwamba nan,

Wasan farko da Fabregas zai ja ragama sa shi ne wanda za su karbi bakunci Feralpisalo a ranar 25 ga watan Nuwamba nan, bayan an kammala wasa na kasa da kasa.

Como itace ta shida a kan teburi da maki 21, bayan buga wasanin  karo 12 a kakar bana.

Fabregas ya koma Como a wata Agustan bara 2022 bayan da ya bar  kulop din Monaco, ya kuma zuba hannun jari a kungiyar ta Italiya tare da abokinsa, Thierry Henry.

Tsohon dan wasan tawagar Ingila da Chelsea, Dennis Wise shi ne shugaban kungiyar, wanda ya koma can a Mayun 2019.

Leave A Reply

Your email address will not be published.