Ododo Ya Zama Zababben Gwamnan Kogi
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta bayyana Ahmed Usman-Ododo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan a Jihar Kogi
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta bayyana Ahmed Usman-Ododo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da a ka gudanar a jihar Kogi.
Ahmed Usman Ododo ya samu ƙuri’a 446,237, wanda ya doke mai biye masa, Muritala Ajaka na jam’iyyar SDP, wanda shi kuma ya samu ƙuri’u 259,052.
sai kuma na ukun su Dino Melaye na PDP , inda ya samu ƙuri’u 46,362.
Hakan na nuna cewa Ahmed Ododo ya doke dukkanin ƴan takarar 18 da suka fafata a zaɓen gwamnan jihar ta Kogi wanda ya gabata a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamban 2023.
Shi dai Usman-Ododo ba kowa ne ya san shi ba gabanin samun nasarar sa da yayi a zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC.a Kogin
A lokacin zaɓen fitar da gwani, Usman Ododo ya doke abokanan takaran sa irin su Shu’abu Audu, Stephen Ochen, Sanusi Ohiare da kuma Smart Adeyemi.
Jihar Kogi na daga cikin jihohi uku da aka gudanar da zaɓe a cikinsu ranar Asabar. BBC Hausa taruwaito a shafinta na intanet cewa:
An haifi Ahmed Usman Ododo ne a ranar 7 ga watan Fabarairun 1982.
Usman-Ododo wanda ɗan ƙabilar Ebira ne da ya fito daga garin Okene, ya yi digirinsa na farko a fannin Akanta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ya kuma yi digirinsa na biyu a fannin kasuwanci a Jami’ar Legas.
Kafin zama ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC, ya kasance babban mai binciken kuɗi na ƙananan hukumomi na jihar, tsawon shekara bakwai da rabi, kuma an yi imanin cewa ya taka rawar gani a gwamnatin gwamna Yahaya Bello mai barin gado.