Tinubu Yayi AlkawarinTallafawa Sarakunan Gargajiya Akan Tsaro

0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin tallafawa sarakunan gargajiya

 

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin tallafawa sarakunan gargajiya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankunansu.
Shugaban wanda ya bayyana goyon bayansa ga rawar da tsarin mulki ya baiwa sarakunan gargajiya, ya ce majalisar dokokin kasar tana kan mafi kyawu matsayi da za ta yi aiki a kan hakan don ganin hakan ya zama doka.

Shugaba Tinubu yayi magana ne a karshen makon da ta gabata  a garin Ondo yayin bikin cika shekaru 70 da haihuwar Oba Victor Kiladejo, Osemawe na masarautar Ondo, a cocin Diocese of Ondo (Anglican Communion) Cathedral Church na St. Stephen.

Shugaban wanda ya samu wakilcin ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce shekaru 17 da suka gabata na Oba Koladejo a kan karagar mulki ana  zaman lafiya.

Hakazalika ya yabawa Sarkin Ondo bisa gagarumin ci gaba da garin ya samu ta fuskar samar da ababen more rayuwa da ci gaban jama’a a zamanin mulkinsa.

Shugaba Tinubu ya bukaci kowa da kowa ya ci gaba da marawa sarkin gargajiya baya domin ganin a ci gaba da zaman lafiya da samun  tsaro a masarautar.
Ya ce Gwamnatin Tarayya  ta yaba da goyon bayan da Oba Kiladejo ya ba hukumomi da  jami’an gwamnati a yankinsa na tsawon shekaru.

Shugaban ya yaba da kudurin fadada iyakokin ayyukan raya kasa a yankin sarakunan gargajiya da kuma talakawansa na gida da waje a shekarun baya.
Shugaba Tinubu ya tuna kusan shekaru ashirin da suka gabata lokacin da sarkin ya janye daga aikin jinya da yake  yi a Legas duk da kasancewar sa kwararre ya hakura da aikin domin ya hau gadon sarautar kakanninsa, a matsayin Osemawe kuma babban mai mulkin masarautar Ondo.domi bada tasa gudunmuwar a masarautar ga al’ummar sa

 

“A bayyane yake cewa shekaru 17 da suka wuce, Mai Martaba Sarkin ya dace a wannan karaga da kyau,

wanda hakan ya tabbatar da cewa sarakunan Ondo, da suke gudanar da ayyukansu a karkashin ikon Allah, ba su yi kuskure ba wajen zaben sa a matsayin Osemawe a 2006.

“A yau, babu wanda ya isa ya kushe aiyukansa domin ganin irin tasirin da mulkinsa ya yi akan al’ummar Ondo Ekimogun. Wanda hakan abune a bayyane ana iya ganin su a ko’ina cikin al’umma kuma sunaamfanar  duk wani abu na kokarin cigaban ɗan adam.

“A bayanin sirri, bari in sake bayyana godiyata gare ku kan wasikun taya murna guda biyu da kuka aiko mani da fatan  alheri bayan nasarar da na samu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, wanda daga bisani   kuma aka rantsar da ni a matsayin shugaban kasar Najeriya.

“Ina addu’a cewa shekarun da ke gaba su zama abin ban mamaki a gare ku, dangin ku, da kuma mutanen masarautar Ondo gaba daya, waɗanda kuka yi wa jagoranci cikin sha’awa tsawon  shekaru 17 da suka shude a zamanin mulkin ka . Muna fatan mulkinku ya ci gaba da zama mai albarka da wadatar Arziki da koshin lafiya.

“Abin da zan iya fatan shi ne a ci gaba da yin hakan kuma mai yiwuwa a samu sauki a karkashin jagorancin Ka ubangiji ya  ci gaba da jagorantar mu ta hanyar da ta dace,” in ji shi.

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya ce shawarar da sarkin Ondo ya baiwa gwamnatinsa yayi tasir matuka kuma yana da kima da kuma mai da hankali kan ci gaba.

“Fatan mu da Addu’ar mu ga mai girma mai martaba ya ci gaba da samun koshin lafiya da hikimar Ubangiji wajengudanar  da shugabancin da ake bukata ga masarautar Ondo da jihar Ondo baki daya.”

“Abin farin ciki ne a gareni na bi sahun sauran ‘yan Najeriya da dama wajen yi wa mai martaba fatan alheri na tsawon shekaru masu amfani ga bil’adama,” in ji shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.