Atiku ya nemi ƴan adawa su dunkule domin su ceto Najeriya, daga Mulkin kama karya

0

Jagoran Yan’adawa a Najeriya ya yi kira ga sauran  jam’iyyun adawa a Najeriya su haɗa karfi da karfe, don tsamo dimokraɗiyyar ƙasar daga komawa zuwa mai bin tsarin jam’iyya ɗaya.

 

Ya kuma jawo hankulan Yan’adawan a kan buƙatar yin hattara game da tsunduma Najeriya, cikin tsarin mulkin kama-karya na jam’iyya ɗaya.

Wata sanarwa da Paul Ibe, mashawarcin ɗan takarar shugaban ƙasar a zaɓen watan Fabrairun 2023 kan harkar yada labarai ya fitar ranar Talata, ta ce Atiku ya yi kiran ne lokacin da ya karɓi bakuncin shugabannin majalisar tuntuɓa tsakanin jam’iyyu ta Najeriya (IPAC).

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar, shi ne ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a farkon wannan shekara, wanda Bola Tinubu ya kayar da shi.

A cewarsa, aikin kare mutuncin dimokraɗiyya a ƙasar nan, ba kawai na mutum ɗaya ba ne.

Ya nunar da cewa hakikanin gaskiya tsarin dimokraɗiyyarmu cikin sauri na komawa zuwa tsarin jam’iyya ɗaya, “kuma tabbas kun sani cewa idan tsarin jam’iyya ɗaya ne da mu, to kawai mu mance da maganar dimokraɗiyya”.

Atiku ya ƙara da cewa “Dukkanmu mun ga yadda jam’iyyar APC ke daɗa mayar da Najeriya zuwa ƙasar mulkin kama-karya mai jam’iyya ɗaya. Idan ba mu zo mun haɗu don kalubalantar abin da jam’iyya mai mulki take ƙoƙarin kafawa ba,  to  babu shakka dimokraɗiyyarmu za ta sha wahala, kuma sakamakon hakan zai shafi hatta zuri’ar da ba a ma haifa ba masu zuwa”.

Atiku Abubakar ya kuma soki lamirin hukumar zabe ta INEC saboda abin da ya kira gudanar da “zabe mafi lalacewa a kasar”.

“Kwanan nan ma a zaben da aka gudanar cikin wasu jihohin kasar uku, INEC ta sake nuna rashin mutunta tsare-tsaren dimokradiyyarmu da ta saba.

“Duk muna iya ganin yadda INEC ta ayyana wani sakamako a jihar Kogi, inda jimillar adadin kuri’un aka kada suka zarce yawan kuri’un da  aka tantance a wata karamar hukuma.

“Ba za mu samu ingantacciyar dimokradiyya ba a yanayin da abin da INEC kawai ta sani shi ne tabbatar da nasarar jam’iyya mai mulki ta kowanne hali.”

wanda hakan ba karamin kalubale ne ba ga cigban demokaradiya a kasa kamar Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.