Kanawa Na Zaman Jiran Jin Sakamako Hukuncin Kotun Daukaka Kara

0

Al’ummar jihar Kano, musamman magoya bayan manyan jam’iyyun guda biyu na jihar, APC da NNPP,

Al’ummar jihar Kano, musamman magoya bayan manyan jam’iyyun guda biyu na jihar, APC da NNPP, sun wayi gari cike da zaƙuwa da zumudi gabanin jin sanar da wani hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, zata yanke nan da ‘yan sa’o’i  kadan  a yau  Juma’a

Hukuncin kotun, wadda ke zamanta a babban birnin tarayya  Abuja, yana da matuƙar muhimmanci ga siyasar jihar, mafi yawan jama’a da harkokin kasuwanci a arewacin Najeriya, kuma ginshiki ne ga makomar siyasar Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon mataimakin gwamna Nasiru Yusuf Gawuna, aƙalla tsawon shekara huɗu nan gaba masu zuwa.

Abba Kabir Yusuf ya garzaya gaban kotun ɗaukaka ƙara ne, bayan kotun ƙorafin zaɓe ta jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba, ta rushe nasarar da ya samu, inda ta ce abokin takararsa na jam’iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna ne halastaccen wanda ya ci zaɓe.

Kotun ta soke sama da 165,000 a cikin ƙuri’un da Abba Kabir Yusuf na jam’iyar NNPP, ya samu bisa hujjar cewa ba su inganta ba, saboda rashin sa hannu da kwanan wata da kuma hatimin hukumar zaɓe kasa.

Jam’iyyar APC ta roƙi kotun ɗaukaka ƙara da ta yi watsi da ƙarar Gwamna Abba KabirYusuf ya shigar.

Takara tsakanin ɓangarorin biyu, na ɗaya daga cikin mafi zafi da aka gani kafin zaɓen 18 ga watan Maris a Najeriya, kuma ga alama har yanzu, yanayin siyasar bai daina tafarfasa ba, wata takwas bayan kammala zaɓe.

Hukumomin tsaro a jihar Kano, tun farkon wannan mako sun ce sun tura ƙarin jami’ai da kayan aiki zuwa manyan fuskokin garin, don hana faruwar tashin hankali, da kuma kare rayuka da dukiyar al’umma, tun kafin sanar da hukuncin na Kotun Daukaka karar a yau juma’a.

Dukkan ‘yan takarar a zaɓen da ya wuce, suna da alaƙa da jiga-jigan ‘yan siyasar Kano biyu, Rabi’u Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje, tsoffin gwamnonin jihar da ke kan ganiyarsu har yanzu, sannan tsoffin manyan aminan juna, kafin su raba sheka a tafiyar siyasa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.