Zan ci gaba da bin kadin zaɓena a Kotun Ƙoli – Abba Kabir Yusuf

0

Zan ci gaba da bin kadin zaɓena a Kotun Ƙoli cewar Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf, da kotun ɗaukaka ƙara ta soke zaɓensa, a ranar Jumma’a da ta gabata ya ce har yanzu yana da ƙwarin gwiwar cewa Kotun Ƙolin Najeriya, za ta dawo masa da nasararsa.

Hakazaliza Abba Kabir ya ce ya yanke shawara tare da masu ruwa da tsaki, inda suka cimma matsayar cewa lauyoyinsa, su shigar da wata sabuwar ƙara a gaban Kotun Ƙoli, don bin kadin haƙƙinsa da na jama’ar jihar Kano da suka sadaukar da lokacin su domin zabensa amatsayin Gwamnan kano.

A cikin wani jawabi da ya yi wa al’ummar jihar Kano,

Abba Kabir ya bayyana takaici da ɓacin rai sa a kan hukuncin kotun na ranar Juma’a.

Jawabin na zuwa ne, sa’o’i kadan bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar, wanda ya tabbatar da hukuncin ƙaramar kotun zaɓe, da ta soke nasararsa tun a watan Satumba. Wanda kuma ta ce Nasir Yusuf Gawuna shi ne halastaccen, ɗan takarar da ya ci zaɓen gwamna na ranar 18 ga watan Maris.

“Ba a yi mana adalci ba, haka kuma ba a yi wa jama’ar Kano adalci ba,” in ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya ce yana da yaƙini, wannan al’amari, koma-baya ne na ɗan ƙanƙanin lokaci da kotun ƙolin Najeriya, za ta warware.

Matakin zuwa kotun ƙoli, shi ne dama ta ƙarshe da gwamnan na jam’iyyar NNPP, yake da ita a ƙoƙarin shari’a da yake yi na kare kujerar da yake kai a jihar kano

Leave A Reply

Your email address will not be published.