Dalilin da ya sa za mu soke rajistar kamfanoni 30,000 a Najeriya – CAC
Dalilin abin da ya sa za mu soke rajistar kamfanoni 30,000 a Najeriya cewar Shugaban- CAC
Hukumar da ke yi wa kamfanoni rijista a Najeriya wato Corporate Affairs Commission (CAC) ta ce za ta rufe kamfanonin akalla basu gaza guda dubu talatin ba sakamakon ba su biyan kuɗin shekara-shekara. kamar yadda doka ta tanada wannan jawabin na zuwa ne a daidai lokacin da Sabon shugaban hukumar ta CAC, Hussaini Ishaq Magaji (SAN),
Yake ganawa da wakilin BBC Hausa in da ya tabbatar masa cewa adadin kamfanonin da lamarin zai shafa ya kai 30,000.
A cewarsa, aikin soke rajistar zai fara ne daga ranar 31 ga watan Disamba mai kamawa.a karshen waannan shekarar 2023
Kamfanoni da sana’o’in da matakin zai fi shafa su ne na shirya tafiye-tafiye, da ‘yan canji, da na haƙar ma’adanai da kuma na lauyoyi a fadin kasar nan.