
Shakira ta biya kasar Sifaniya tarar kudi fam miliyan 6.5
Shakira ta cimma yarjejeniya da masu shigar da kara na kasar Sifaniya domin sasantawa kan tuhumar ta da almundahanar biyan haraji, a daidai lokacin da ake shirin fara shari’arta.
Mawakiyar yar kasar Colombia Shakira ta biya tarar kudi Yuro miliyan 7.5m – masu gabatar da ƙara sun so a daure ta tsawon shekara takwas, sannan a ci tarar ta Yuro miliyan 23.8, idan aka same ta da laifin da ake zargin ta da aikatawa.
Ta fuskanci zargin almundahana a kan kuɗi Yuro miliyan 14.5 a wata kotun da ke Barcelona.
Shakira, wadda ta sha musanta aikata wani laifi, ta ce ta cimma yarjejeniyar ne saboda da ƴaƴanta.
A cikin wani dogon bayani, ta ce ‘ya’yanta “ba sa son ganin mahaifiyarsu ta sadaukar da rayuwarta a kan wannan rikici”.
A baya dai, mawaƙiya Shakiran ta yi watsi da yarjejeniyar da masu gabatar da kara suka gabatar, a maimakon haka ta zaɓi zuwa kotu.
Rikicin ya shafi kasar da take zaune a ciki a tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2014, inda masu gabatar da kara suka ce ta zauna a Sifaniya amma ta lissafa zaman a wani wuri.
A karkashin dokar Sifaniya, mutanen da suka shafe fiye da wata shida a kasar, ana daukar su a matsayin mazauna ne ta fuskar dalilai na biyan haraji. Amma Shakira ta musan ta cewa Sifaniya, ba ta kasance mazauniyar Sifaniya a wannan lokacin ba.